Jirgin da ke jigilar gawar ya iso da misalin karfe 3:39 na rana. a ranar Juma'a, 5 ga Janairu, 2024.
An kawo gawar marigayi Gwamnan daga kasar Jamus, inda ya rasu. Matarsa, Betty Anyanwu-Akeredolu, da ’ya’yansa, da ’yan uwansa ne suka karbe gawarsa a karkashin jagorancin Farfesa Wole Akeredolu, wanda kaninsa ne.
Marigayi Akeredolu ya mutu ne a ranar 27 ga Disamba, 2023, bayan ya yi fama da cutar daji ta prostate.
From ISYAKU.COM