Da ɗumi: Mata sun fusata, sun banka wa gidan basarake wuta a Bokkos jihar Arewa


Wasu gungun mata da suka fito zanga-zanga da tsakar rana yau Jumu'a sun ƙona gidan hakimin garin Bokkos, ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa matan sun banka wuta a gidan basaraken mai suna, Michal Monday Adanchi, da misalin ƙarfe 12:30 na rana. Legit Hausa ya wallafa.

Majiyar ta ce matan sun kona gidan ne biyo bayan damke wasu mazauna yankin bisa zarginsu da hannu a kashe-kashen da aka yi a Bokkos kwanan nan.

Jaridar Daily Trust ta tattaro majiyar na ƙara bayanin cewa gidan basaraken da kuma ofishin da yake gudanar da harkokin shugabanci sun ƙone ƙurmus.

Majiyar ta ce:

"Lamarin dai ya fara ne a ofishin ‘yan sanda inda suka nuna bacin ransu bisa kame wasu daga cikin mazauna garin Bokkos.
"Bayan sun bar ofishin yan sanda sai suka wuce gidan basaraken, suka nuna ɓacin ransu cewa ya siyar da mutuncinsa. Suna zuwa gidan suka banka masa wuta."

The Nation ta ruwaito cewa tuni dakarun rundunar Sojin Najeriya suka isa wurin kuma har sun tarwatsa matan da ke wannan zanga-zanga.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce zai kira DPO na yankin ta wayar tarho gabanin ya yi magana da ƴan jarida kan lamarin.

Rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Alhamis ta tabbatar da cafke wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a hare-haren baya bayan nan a kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN