Da duminsa: Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma tare da jama'arsa a jihar Arewa


Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga, Safiyanu Isah.

 An yi garkuwa da Isah ne a daren Litinin, 1 ga watan Janairu, 2024, a kauyen Ningo, dake kan titin Akwanga-Andaha.

 Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kamal Dauda Rija, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sace shi ne tare da wasu, ciki har da wani fitaccen mai bayar da agaji a karamar hukumar, Adamu Umar, wanda aka fi sani da Maccido.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sauran hukumomi, sun yi gaggawar fara farautar wadanda suka yi garkuwa da su domin ganin an sako wadanda aka sace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN