Amarya, sirikinta, mata biyar da wasu 6 sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar Neja


Mutane 13 da suka hada da wata sabuwar amarya, wasu mata biyar, sirikinta, da wasu mutane shida sun mutu a wani hatsarin mota kusa da Lukoro a Edati, jihar Neja. 10 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun kammala karatu ne a kwalejin kimiyyar lafiya ta Sultan Abdulrahman College of Health Gwadabawa, sun hallara ne domin murnar daurin aure tsakanin wani wanda ya kammala karatun digiri, Umar Jibril Muhammad da wata dalibar lafiyar hakori mai suna Amina. Mummunan hatsarin da ya afku a yammacin ranar Juma’a 26 ga watan Junairu, 2024, an danganta shi da gudun wuce gona da iri.  Hadarin ya hada da wasu motoci guda biyu:  Toyota Corolla Mai kalar toka da ta taso daga Mokwa zuwa Bida da wata motar bas kirar Nissan ta kasuwanci da ta taso daga Minna babban birnin jihar Neja zuwa Ogbomosho a jihar Oyo. Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja, Tsukwan Kumar, ya ce hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar wasu manya mata takwas, da manya maza hudu, da kuma yaro namiji daya. Ya kara da cewa manya mata hudu, babba namiji daya, yaro namiji daya, da mace daya sun samu munanan raunuka. An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Bida domin kula da lafiyarsu, yayin da aka kula da gawarwakin wadanda suka mutu. An mika mutanen tara ga ‘yan uwansu a wurin da hatsarin ya afku bayan an tantance su, sannan an kai sauran hudun zuwa babban asibitin Kutigi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN