Al’ummai masu zuwa ba za su da wani zabi illa biyan bashin da ake ciyo masu a yanzu – Obasanjo


Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya sake bayyana rashin amincewa da basussukan da Najeriya da wasu kasashen Afirka ke ciyowa.

 Da yake jawabi a wajen wani taro da masu bayar da lambar yabo ta Future Africa Leaders Foundation 2023, wani shiri na Fasto Chris Oyakhilome, Obasanjo ya bayyana cewa da matakin rashin tattalin basussukan da aka biya a baya wasu aka yafe wa Najeriya, zai yi wuya wata gwamnati ta samu makamancin irin wannan damar a nahiyar Afrika.

 Ya bayyana cewa bashi wani tarko ne da babu wani mutum ko al’umma da bai kamata su fada cikinsa ba domin ya zama albatu kan kowace irin tattalin arziki.

 Obasanjo wanda ya bayyana cewa shugabanci shine matsala ta farko da nahiyar ke fuskanta, ya kara da cewa "al'ummai masu zuwa ba za su da wani zabi illa biyan bashin da ake bin kasashen nahiyar a halin yanzu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN