Korafi zuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi - Muhammed Bawah


Assalamu Alaikum, da fatar kuna lafiya. Mu na son a mika kukanmu ga Gwamnan Jaharmu na Kebbi; Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu da ya taimaka ya biya tsofaffin ma'aikata masu PENSION ARREARS hakkin su. Pension Arrears yana faruwa ne wajen tsaikon samun clearance daga Ma'aikatar Ma'aikaci da Audit da Finance (incorporated/audit depts) da ofishin Kwamiti na Audit ( Kwaido committee).

Dalilin tsaikon sai ma'aikaci ya rasa albashi a ma'aikatar da yayi retire haka kuma ya rasa Pension don ba'a tantanceshi ba wajen Kwaido committee. Hakke ne babba a kan Gwamnatin Jaha.

2: Mu na son akai korafi ga Gwamna na a biya Iyayen daliban makarantun gaba da Sakandare, kudin registration na 2022/2023 session da suka biyawa 'yayansu watau 'registration fees refund'.

Wannan zai taimakawa Iyaye su kwantsama wajen biyawa Yaran su sabon registration fees na 2023/2024 session cikin wannan sabuwar shekara.

Haka mu na k'ara kuka na cewar Gwamna ya duba ya biya kudin gabadaya ko kashi biyu cikin uku ( 2/3 ) na kudin maimakon rabi (1/2 ) saboda yanayin da ake ciki. Akwai matsatsin rayuwa, ga shi wa su Iyayen na da Yara fiye da daya.

Mungode, Allah Ya sa mu dace. Ya bamu sa'a.
Allah Ya zannadda Jaharmu ta Kebbi da K'asarmu ta Najeriya lafia da bunk'asar arziki.

Amin Summa Amin.
Nagode.

Muhammed Bawah

SANARWA

Wannan rubutun na sama ba alhakin shafin labarai na isyaku.com bane. Hakkin mallakin marubucin ne Muhammed Bawah

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN