Yanzu-Yanzu: Yara, da mata sun mutu yayin da Jirgin wuwa ya kife a rafin Niger


Mutane da dama ciki har da mata da yara, a cikin wani jirgin ruwa da ba a tabbatar da sunansa ba ana fargabar sun mutu lokacin da jirginsu ya kife a Rafin Niger. Legit Hausa ya wallafa.

A cewar The Punch, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi, 7 ga watan Disamba, a yayin da aka gano wasu yan Najeriya na ceto wadanda abin ya faru da su a gabatar Onitsha.

An gano hakan na cikin wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta a ranar Lahadi.

A lokacin rubuta wannan rahoton, ba a riga an tabbatar da adadin wadanda suka rasu ba, amma an gano fasinjojin sun fito ne daga jihar Kogi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya kara da cewa a halin yanzu an shawo kan lamarin.

Kakakin yan sandan ya ce jami'an sojojin ruwa sun amsa kirar neman dauki cikin gaggawa daga suka samu daga yankin.

Wani sashi na sanarwarsa ta ce:

"Binciken farko ya nuna cewa jirgin ya fito ne daga Jihar Kogi, yana dauke da kayayyaki da fasinjoji kafin abin bakin cikin ya faru."
Ikenga ya ce kawo yanzu ba a gano sanadin afkuwar hatsarin, ya kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN