Wata damisa ta cinye dan yawon bude ido a gidan ajiye dabbobi

 

Wani damisa ya cinye wani mutum a gidan namun dajin jama'a.

 Ma’aikatan tsaftace gidan ne suka gano gawar mutumin da damisa ya ci rabin gawar a gidan ajiye namun daji na Sherbagh da ke lardin Punjab na Bahawalpur a kasar Indiya.

 Ana tunanin cewa mutumin ya yanke shawarar haura shinge zuwa wurin dabbobin, amma abin da ya faru a baya ya zama abin ban mamaki.

 Sai da ma’aikatan shara suka hango daya daga cikin damisa guda uku da ke cikin kejin yana zagayawa da takalmi a bakinsa sannan aka tsinci gawar.

Har yanzu dai ba a san asalin wanda damisa ya kashe ba, kuma babu wani dangi da suka fito domin neman abin da ya rage na gawar, amma a sakamakon haka an rufe gidan namun dajin. Yayin da aka dauke ragowar gawar zuwa wani asibiti.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN