Kayya: Yadda wata mata ta kama saurayi yana lalata da Zakara turmi tabarya

'

 Yan sanda a Adamawa sun kama wani matashi dan shekara 17 mai suna Lawali Mori, mazaunin Viniklang, karamar hukumar Girei, bisa laifin yin lalata da zakara.

 Kamen dai ya biyo bayan korafin da wata Esther Dimas da ke zaune a Viniklang ta yi wa 'yan sanda, bayan ta kama wanda ake zargi da aikata laifin.

 Lokacin da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya kara bayyana cewa ya yi lalata da zakara amma bai iya bayar da dalilan da ya sa ya aikata haka ba.

 Da yake tabbatar da kamun, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, yayin da yake nuna damuwarsa, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN