Yanzun nan: "Ba zamu haƙura ba" Sarkin Musulmi ya maida zazzafan martani kan jefa wa Musulmai bam a Kaduna


Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya buƙaci mahukunta su yi adalci ga waɗanda harin bama-baman soji ya shafa a kauyen Tudun Biri.

Sama da mutane 120 ne suka rasa rayukansu sakamakon jefa bam har sau biyu da jirgin sojojin kasa ya yi a taron Maulidi a kauyen da ke ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.  Legit Hausa ya wallafa.

Sarkin Musulmin ya nemi a yi wa mutanen adalci ne yayin da yake jawabi a wurin bikin cikar Sarkin Jema'a na 11, Muhammad Isa Muhammad (CON), wasu shekaru a karagar mulki.

Daily Trust ta tattaro cewa yayin da yake jawabi a fadar Sarkin da ke Kafanchan, Sultan ya ce ba zasu haƙura ba, zasu ci gaba da matsa lamba har sai an yi adalci kan lamarin.

"Ba mun zo nan taya Sarki murna kaɗai bane, mun zo ne mu yi wa masarauta addu'a tare da rayukan bayin Allah da aka kashe a jihar Kaduna."

"Zamu ci gaba matsa lamba kan wannan lamari har sai mun ga an yi wa mutanen da ibtila'in ya shafa adalci," in ji Sultan.

Da yake martani, babban hafsan hafsoshin sojin kasa, Janar Christopher Musa ya bayyana abin da ya faru a Kaduna a matsayin abin takaici da nadama.

“Nauyin da ke kanmu shi ne mu kare rayukan ’yan kasa, za mu dauki kwakkwaran mataki don ganin irin wannan abu bai sake faruwa a ko’ina a kasar nan ba."

"Shugaban ƙasa ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan abin da jawo yin wannan kuskuren," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN