Kungiyar KAGAF (KAURAN GWANDU ADVOCACY FORUM) Karkashin jagorancin Uwar gidan maigirma Gwamnan Jahar Kebbi Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris ta baiwa masu lalura ta musamman kyautar JAMB form guda hamsi (50) domin suma su samu gurbin karatu a makarantu na gaba ga sakandare.
Wannan na zuwa ne a ranar 3 ga watan Disamba wanda ranace ta tunawa da masu bukata ta musamman (International persons with disabilities day) na Duniya.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Coordinator na KAGAF Mansur Sarki Gwandu, inda yake kara yabawa Matar Gwamnan bisa ga irin muhimmiyar rawar da take takawa wurin bunkasa harakar ilmi da kuma taimaka wa matasa wajen dogaro da ka a jahar Kebbi.
From ISYAKU.COM