Daraktan DSS, Bichi ya handame kudaden tallafin ma'aikatansa? gaskiya ta bayyana


Hukumar DSS ta yi fatali da jita-jitar cewa daraktan hukumar, Alhaji Yusuf Bichi ya handame kudaden rage radadi na ma'aikata. 

Wani mutum mai suna Jackson Ude shi ya yi wannan zargi inda ya ce Bichi ya yi sama da fadi da tallafin kudaden ma'aikatan hukumar.  Legit Hausa ya wallafa.

Daraktan yada labarai na hukumar, Dakta Peter Afunanya shi ya yi wannan martani a yau Asabar 2 ga watan Disamba a Abuja. 

Afunanya ya ce Ude a kullum kokarin bata sunan Bichi ya ke a matsayin mai cin hanci da rashawa inda hukumar karyata 

Ya ce hukumar ta yi bincike a baya kan irin wadannan zarge-zarge inda ta tabbatar karairayi ake yi wa Bichi, The Nation ta tattaro. 

/Sanarwar ta ce: 

"Hukumar DSS ta samu labarin zargin cin hanci kan Bichi da wani Jackson Ude ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Hukumar ta tabbatar da wannan magana karya ce kuma babu wani daga cikin ma'aikatanta da ya handame kudaden tallafi. 

"Babu wasu kudaden tallafi da aka turo wa hukumar kuma da zarar an turo kowa zai samu kasonshi kamar yadda aka saba." 

Afunanya ya ce Bichi ba irin wannan mutumin ba ne saboda ya damu da walwalar ma'aikatansa har da wadanda su ka yi ritaya, cewar Platinum Post. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN