Yadda Tururuwa suka fara lullube jariri da aka haifa aka sa a leda aka jefar makale da cibiyarsa a birnin Minna jihar Neja


Mazauna unguwa sun ceto wani yaro dan kwana daya da aka yi watsi da shi a unguwar Tayi da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

 Mazauna yankin sun ce an gano jaririn ne sa’o’i kadan bayan da wani da ba a san ko su wanene ba suka yasar da shi a yammacin ranar Asabar, 2 ga Disamba, 2023.

 Daya daga cikin mazauna unguwar, Aliyu Bala Ibrahim, ya ce an nade jaririn ne a cikin laida tsirara, aka bar shi.

 “Wannan yaro (watakila ‘yan sa’o’i ne da suka wuce aka haife shi) an same shi a yashe a kusa da gidana a nan unguwar Tayi, Minna, Jihar Neja.  An lulluɓe jarrin da laida kuma an bar shi ba tare da sutura ba," in ji shi.

 “ Tururuwa sun fara rarrafe a jikin shi kafin a same shi.  Wannan shi ne yanayi mafi ban tausayi da na taɓa gani a rayuwata.  Yakamata a zartar da hukuncin kisa a kan mutanen da suka aikata hakan.”

 “Har yanzu igiyar cibiya tana makale da jaririn.  Ina tsammanin an haife shi sa'o'i kadan da suka wuce.  Ba su ma yi masa wanka ba.  Sai kawai suka wanke jinin jikinsa suka jefar da shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN