Tsohon Shugaban APC ya haddasa fitina, ya fallasa yadda aka kashe miliyoyin naira saboda a doke PDP, duba adadin kudin


A wajen nuna kokarin da ya yi a ofis, Adams Oshiomhole ya fadi yadda jam’iyyar APC ta kashe miliyoyi domin karbe jihar Kwara.

Da yake jawabi wajen kaddamar da littafin Salihu Lukman, Adams Oshiomhole ya ce uwar jam’iyya ta kashe N800m domin a doke APC a Kwara. Legit Hausa ya wallafa.

Jam’iyyar APC ta batar da wadannan kudi ne da nufin hambar da daular Bukola Saraki wanda ya sauya-sheka daga APC zuwa PDP a 2018.

Bayan maganar da tsohon shugaban na APC ya yi, Legit ta samu labari jam’iyyar PDP ta bukaci a kama APC da laifin sayen kuri’u yayin zabe.

Jam’iyyar hamayyar ta soki yadda APC tayi bindiga da daruruwan miliyoyi domin kurum tayi nasara a jihar Kwara a zaben da aka yi a 2019.

A karshe Abdulrazaq Abdulrahman da ‘yan takaran APC sun samu galaba a Kwara.

Daily Trust ta rahoto Ibrahim Akaje yana neman a dawo masa da kudin da ya kashe wajen sayen fam domin shiga takarar majalisar tarayya.

Akaje ya bukaci a maido masa kudin da ya batar a 2019 ne bayan jin Oshiomhole yana cewa sun maidawa masu neman takara kudinsu.

Tsohon kwamishinan kasuwanci, kirkire da fasaha na jihar Kwara ya yi magana a Facebook, yana tambayar ina kudin na su suka shiga.

Da jaridar ta tuntubi shugaban APC a Kwara, Alhaji Tajudeen Folaranmi Aro, ya ce yana wajen taro ne a lokacin, zai yi magana daga baya.

‘Dan siyasar ya ce tun da NWC ta ba jam’iyya ta reshen Kwara N800m da kuma N220m na kudin masu sayen fam, dole kudinsu su dawo.

An samu labari Salihu Muhammad Lukman ya ce da farko Shugaba Bola Tinubu da APC sun samu karbuwa sosai wajen ‘yan Najeriya.

Jigon na APC ya ce yanzu an koma gidan jiya a jam’iyyar APC, sabon shugaban kasar ya koma irin mulkin da Muhammadu Buhari ya yi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN