Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana shirin taron addini a arewa, sun kashe sama da mutane 15


Yayin da ake shirin bukukuwan kirsimeti, ƴan bindiga sun halaka mutane aƙalla 16 a sabon harin da suka kai ƙauyen Mushu, ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato. Legit Hausa ya wallafa.

Mai magana da yawun Operation Safe Haven, rundunar sojin haɗim guiwa mai aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Kaftin James Oya ne ya tabbatar da haka ga Premium Times.

A cewar Kaftin James, maharan sun kai wannan hari kauyen ne ranar Asabar a daidai lokacin da mutane suka kwanta bacci.

Ya ƙara da cewa:

"Biyo bayan samun labarin kai harin, an kara girke jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana a yankin domin dakile duk wani yunƙuri na karya doka da oda."

"An samu tashin hatsaniya bayan kai harin amma zuwa yanzun jami'an tsaro sun shawo kan lamarin."

Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin wanda ya yi ajalin rayuka, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci da kuma rashin tausayi.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gyang Bere, ya fitar, Mutfwang ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Mista Bere ya ce gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin, inda ya bukaci al’ummar jihar da su sanya ido, kana su kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro domin daukar mataki cikin gaggawa.

Ya kuma nuna rashin daɗinsa kan yadda ire-iren waɗannan maharan ke cutar da mutane da lalata dukiyoyi ba tare da sun fuskanci hukunci ba., cewar Daily Trust.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN