NDLEA ta kama dillali da ke sayarwa 'yan bindiga kwayoyi a Zamfara da Kebbi


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama Agu Amobi, wani dan kasuwa mazaunin Qatar, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, da ke Lagos, bisa zargin safarar kwayoyi.

Cewar sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Femi Babafemi, mai magana da yawun NDLEA, ya ce an kama wanda ake zargin ranar Asabar yayin da ya ke kokarin ketarewa zuwa Doha ta jirgin Qatar Airways. Legit Hausa ya wallafa.

Ya ce an kama Amobi da kilo 1.30 na tabar wiwi da aka nade a jakar kayan abinci.

Babafemi ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin a Qatar ya ke zaune sama da shekara 10 kuma ya na siyan kwayoyi daga Enugu ya kai Doha don ya samu ya biya kudin makarantar yaransa uku.

A wani makamancin rahoton a rana guda, Uchegbu Obi ya shiga hannu bayan an kama shi da kwayar tiramol da ta kai 72,000 a MMIA.

An ruwaito cewa Obi yayi kokarin aika kwayar daga Lagos zuwa Kano.

Hukumar ta kuma tabbatar da kama mutum uku Musa Sani, Mohammed Ibrahim da kuma Adamu Usman da kurkura dauke da wiwi da nauyinta ya kai 15 da kuma kwaya har guda 128,500 a Jihar Yobe.

Hukumar ta kuma wani mai shekaru 45 Yusuf Yahaya a jajeberin Kirismeti a hanyar Lagos zuwa Ibadan da kilo 31 na tabar wiwi a wata motar haya da ta taso daga Ibadan, jihar Oyo, zuwa Jihar Kebbi.

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun kwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun kwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN