An kama wani fitaccen barawo da ake zargin ya kware wajen sata a Masallatai a birnin Mombasa na kasar Kenya, tare da tilasta masa cin danyen barkono.
A cewar mawallafin yanar gizo na kasar Kenya, Cyprian Nyakundi, an kama wanda ake zargin a Masallacin Mkanyageni ranar Talata, 26 ga Disamba, 2023.
“An kama shahararren barawo mai suna Wa Viatu a Masallatai daban-daban a Mombasa babban birnin kasar Kenya. Jiya an kama shi dumu-dumu a Masallacin harin Mkanyageni kuma hukuncin da aka yi masa ya kunshi duka da tilasta shi cin danyen barkono,” ya rubuta.
From ISYAKU.COM