Budurwa ta yi amfani da bindigar dan sanda ta harbe shi har lahira


Wani dan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Cosmas Ugwu, ya gamu da ajalinsa bayan budurwarsa ta harbe shi har lahira.


 An kashe Ugwu ne a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, bayan  budurwarsa mai shekaru 23, wacce aka bayyana sunanta da Amanda Uchechi Ugo, ‘yar asalin karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo ta harbe shi.


 An tattaro daga majiya mai tushe cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Disamba 26 a yankin Ezinihitte.


 Marigayin ya yi fada da budurwar tasa a dakin da ke ofishin ‘yan sanda, kuma ana cikin rikicin ne sai yarinyar ta kai hannu ta dauki bindigar marigayin, ta ja bindigar ta harbe shi har sau uku.

An ce jami’an da ke bakin aiki sun gudu ne bayan da suka ji karar harbe-harbe har sau uku. 


 Wata majiya ta ce a ranar Alhamis: “Lokacin da jami’an ‘yan sanda suka shiga dakin daga baya don ganin abin da ke faruwa, sai suka tarar da Kofur Ugwu a kwance a cikin jininsa.  Yarinyar ta harbe shi har sau uku a kirjinsa da kuma hannun hagu.  Nan take aka garzaya da shi Asibitin Evergreen da ke Ezinihitte, inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa.”


 “A zahiri babu wanda ya san abin da ya faru tsakanin su biyun, amma yadda yarinyar ta yi nasarar amfani da bindigar ‘yan sanda cikin nasara har yanzu abin mamaki ne ga mutane da yawa.  WataĆ™ila Ugwu ne ya koya mata.”


 An ajiye gawar jami’in da aka kashe a dakin ajiyar gawa na Obizi yayin da ake ci gaba da bincike.


 Wanda ake zargin tana hannun ‘yan sanda.


 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan sanda na yin duk abin da ya dace domin gano hakikanin abin da ya faru.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN