Gwamnatin jihar ta kuma sanar da cewa gwamnan bai mutu ba a Legas kamar yadda aka ruwaito.
Akeredolu ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga Disamba, 2023, yana da shekaru 67.
An yi ta yada cewa gwamnan ya rasu ne a wani asibitin Legas bayan ya sha fama da ciwon daji, da kuma cutar sankarar jini.
Sai dai kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Ondo, Bamidele Ademola-Olateju, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bayyana yadda gwamnan ya rasu.
Yace; "Akeredolu ya rasu ne yayin da yake jinya a Jamus. Ya fuskanci matsalolin da suka taso daga ciwon daji na prostate.
"Iyalan da gwamnatin jihar za su fitar da karin bayani game da shirye-shiryen jana'izarsa."
From ISYAKU.COM