Ta faru: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano


Rahotanni da ke zuwa daga yankin unguwa uku da ke karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano sun kawo cewa wata matar aure ta hada kai da mijinta inda suka kashe abokinsa. Legit Hausa ya wallafa.

Kamar yadda @Ussyy___ ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, daya daga cikin yan uwan mamacin mai suna Sunusi Abdullahi Gwarando ya tabbatar da faruwa lamarin.

A cewarsa, Gwarando ya ce tuni matar ta amsa laifinta inda ta jaddada cewar ta caka masa wuka ne a wuya da kahon zuciyarsa. Ya ce:

Ɗan uwana ne na jini kuma ƙani yake a gare ni.

"Ya gamu da ajalin sa ne a jihar Kano karamar hukumar Tarauni cikin unguwa uku.

"Abokin sa da matar abokin nasa, su suka shirya komai da kan su, kuma matar ta amsa yi masa kisan gilla..!

"Matar ta amsa da bakin ta ita ta caccakka masa wuka a wuya da kahon zuciya da kuma gefen cikin sa har ya mutu..!

"Yanzu haka mutum uku suna hannun jami'an tsaro mijin da matar da kuma wanda ya tattare shi ya sa likafani da sunan ya masa wanka."

Har ila yau, wani bidiyo ya bayyana a dandalin Instagram inda Malam Hafizu Gorondo, mahaifin marigayin mai suna Nafiu ya yi bayani kan rasuwar dan nasa.

Malam Hafizu wanda ke zaune a jihar Bauchi ya bayyana cewa abokin dan nasa ne ya kira shi daga jihar Kano cewa Allah ya yi masa rasuwa sakamakon aikin da aka yi masa a kwanakin baya.

Ya bayyana cewar da daddare aka sanar da su labarin mutuwar kuma ko kafin su isa garin Kano daga jihar Bauchi sun tarar an nade marigayin a cikin likafani bayan an sanar masu cewa ciwon shi ne ya tashi kuma ya yi ajalinsa.

Sai dai mahaifin yaron ya ce har ransa bai gamsu da hakan ba saboda yanayin yadda suka riski abubuwa bayan isarsu Kano.

Ya ce:

"An yi wa dana kisan gilla ne ba rashin lafiyar da ta same shi kwanakin baya ba ne sanadin.

“Da farko sun yaudare ni da cewar ciwon sa ya tashi kuma Allah ya yi wa Nafiu rasuwa, sai suka tambaye ni yaushe za mu masa sallah jana’iza sai nace musa karfe 10.

"Bayan na isa Kano har karfe 7 na safe ban fahimci akwai wani abu ba sai da muka sake kallon gawa sai muka ga jini na ta zuba.

“Anan na bukaci a bude gawar sa mu gani, ina budewa sai naga kota ina a wuyan sa an caccaka masa wuka.

"Shine muka tafi wajen ‘yan sanda suka zo suka dauki hotuna da jawabai kuma sun kama wadanda ake zargi da hannu a kisan."

Sai dai kuma, zuwa yanzu ba a samu wata sanarwa daga rundunar yan sandan jihar Kano a kan wannan al'amari ba.

Ya kuma tabbatar da cewar matar ta sanar da hukumar yan sanda cewa ita ta aikata masa wannan danyen aiki.

A cewarsa bayan ta aikata kisan kan, ta sanar da mijinta inda shi kuma ya nemo malamin karya suka nade shi da sunan yi masa sutura. Ya kuma ce sun ga digo-digon jini a wurare da dama a gidan.

Ga bidiyon hirar da aka yi da Mahaifin marigayin a kasa:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN