An bizine gawar da aka kashe aka kone ta a shiyar Sakita da ke Unguwar bayan Oando a garin Birnin kebbi.
Jami'an hukumar Hisbah na jihar Kebbi suka jagoranci jana'izar gawar bisa abin da ya sauwaka na ka'idodin addinin Musulunci duba da gawar ta fara rubewa har ta farawa wari.
Bayanai sun yi nuni da cewa ana kyautata zaton an kashe gawar ne kwanaki uku da suka gabata kafin a koneta.
Har zuwa lokacin binne gawar ranar Alhamis 21/12/2023 babu wanda ya shada gawar balle dalilin da ya sa aka kasheta.
From ISYAKU.COM