Mai girma Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce ya gano wasu likitoci da gwamnatin jiharsa ke biya albashi duk da sun tsere sun koma aiki a kasashen waje. Legit Hausa ya wallafa.
Otti ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi a wani taron majalisar kiwon lafiya ta jihar a ranar Alhamis a Umahia inda ya ce likitocin na karbar albashi duk da sun san sun ajiye aiki.
The Punch ta ruwaito gwamnan na nuni da cewa tafiya ci-rani da likitoci ke yi zuwa kasashen ketare ya jawo koma baya a fannin lafiyar jihar, ya kuma yi alkawarin inganta albashi da walwalar likitoci.
Ya ce:
"Mun yanke shawarar biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya da wuri, da kuma bunkasa walwalarsu don kawo karshen zuwa ci-rani da suke yi kasashen waje."
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kara daukar wasu ma'aikatan kiwon lafiya don bunkasa fannin lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce:
"A shirinmu na mayar da tsarin aikin gwamnati zuwa na zamani a jihar Abia, mun gano wasu likitoci da har yanzu suke karbar albashi duk da sun ajiye aikin, sun tafi turai ci-rani.
"Wannan laifi ne da dole hukumomin da abin ya shafa za su dauki mataki, abin da yanzu muka mayar da hankali kansa shi ne kara yawan likitoci da bunkasa rayuwarsu."
Ministan ilimi, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Abia, Dr. Ifenyiwa Uma-Kalu, ya ce akwai bukatar jihohi su samar da gine-ginen cibiyoyin kiwon lafiya.
Hukumar gudanarwar asibitin kwararru na jihar Kogi ta sanar da cewa har yanzu likitoci ba sa neman aiki a asibitin duk da bude kofar da suka yi.
A cewar Dr. Ish Adagiri, ya ce likitoci na ajiye ayyukansu a Najeriya suna tsallakewa zuwa kasashen ketare don yin aiki da zummar tara makudan kudade.
From ISYAKU.COM