Ta faru: Alkali ya ba da sammacin kama Konturolan CBN, ya ba da umarnin siyar da kadarar bankin na wata jihar arewa

 

Wata babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos babban birnin jihar, ta bayar da umarnin kwace wata mota mallakin babban bankin Najeriya (CBN) kan wata kara tsakanin wani lauya mai suna John Eche Okpe da babban bankin kasar.

 Mai shari’a ND Shaseet ya ba da umurnin, kuma kadarar da aka kama wata motar Innoson IVM Double Cabin ce mai lamba KUJ696DD ce. Daily trust ya rahoto.

 A ranar Asabar ne aka bai wa ‘yan jarida sanarwar kwace motar a garin Jos.

 A shari’ar mai lamba PLD/J397/m/2023, Okpe ya samu hukunci a kan gwamnatin tarayya da wasu hukumominta tare da neman aiwatar da hukuncin ta hanyar shigar da kara a kan CBN.  Odar garnishee nisi shine N10m kamar yadda alkali ya bayar a ranar 1 ga Nuwamba, 2023.

 Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da Kotu ta ba babban bankin Najeriya wannan umarni, ta ki bin umarnin, wanda hakan ya sa aka kwace kadarorin.

 Sanarwar ta ci gaba da cewa, adadin kudin da aka bayar da takardar a yanzu ya kai N12,206,900, gami da kudaden shari’a da aka kashe, inda ta ce za a sayar da kadarorin ne bayan kwanaki biyar, daga ranar 22 ga Disamba, 2023.

 Alkalin kotun ya bayar da sammacin kama Konturola na CBN na jihar, Mista Jonah Akama, bisa rashin bin umarnin kotu a cikin karar.

 Sammacin kamun da aka bayar ga manema labarai a Jos mai dauke da sa hannun mai shari’a N.D. Shaseet ya karanta cewa duk dan sandan da ya ci karo da Akama ya kama shi.  An yi nuni da cewa, sammacin kama shi ya biyo bayan gazawar Akama a gaban kotu kan karar da Okpe ya shigar.

 Da aka tuntubi dan jin ra’ayinsa, Lauyan CBN, A. A. Adewole, ya ki cewa komai kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN