Zargin satar biliyoyi: Diezani ta roki shugaba Tinubu, ta yi zargin ta ba wani Gwamnan arewa ajiyar dala biliyan 9


Tsohuwar ministar man fetur a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Ebele Jonathan, wadda ta yi gudun hijira zuwa kasar Birtaniya saboda tsoron EFCC, Diezani Alison Maduekwe ta roki gwamnatin Najeriya da ta yi mata sassauci.


 Wata sanarwa da EFCC ta fitar ta ce, Misis Diezani, wadda rahotanni ke cewa tana fama da ciwon mataki na biyu na cutar kansa, tana rokon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba ta dama ta dawo Najeriya ta yi bayani kan tuhumar karkatar da makuddan kudade a lokacin da take kan mukami.


 Misis Diezani tana amsa tambayoyi daga manema labarai a birnin Landan bayan ziyarar jinya.  Tsohuwar ministar man fetur da ake zargi da satar kudaden Najeriya da suka kai biliyoyin daloli, ta bayyana cewa a yanzu haka a shirye take ta tofa albarkacin bakinta game da kudaden da ake zargin ta karkatar yayin da take rike da mukamin ministar mai.


 ‘’Ni Kirista ce kuma Yar "born again"  kuma a halin yanzu ina fama da ciwon daji a mataki na biyu, wanda likitan Burtaniya ya ba ni shawarar in ci gaba da shan magani har tsawon rayuwata.  Hakika, babu É—an adam kamiltacce, amma wani lokaci Allah MaÉ—aukakin Sarki ya Æ™yale wasu ababe su faru.

 An zarge ni da almubazzaranci a lokacin da nake Ministan Man Fetur, gaskiya ne!  amma ina son Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ’yan Najeriya su gafarta mini na dawo gida in ba da gudunmawata domin rayuwa ta wucin gadi ce,” wata sanarwa da EFCC ta fitar ta ce Diezani ta yi wannan cikin kuka.


 Sanarwar ta EFCC ta ci gaba da cewa;

 “Mijina da dukkan ‘yan uwana da suka hada da Lauyan Najeriya da ke da zama a Burtaniya sun san dangantakara da Dauda Lawal Dare, Gwamnan Jihar Zamfara a yanzu wanda na ba wa sama da dala biliyan 9 amanar tsaro a lokacin yana Babban Darakta na Bankin First Bank.  Nigeria PLC.

 Abin takaici, yanzu ya kai ga cewa Mista Dauda Lawal ba ya karbar kiran wayata, har ma ya yi aiki tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Birtaniya don sa ido a kaina, watakila yana neman ya danne kudin da na damka masa idan na mutu,” inji ta. Kamar yadda LIB ta rahoto.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN