Jami'an hukumar Hisbah na jihar Kebbi sun sami yan mata yara kanana guda biyu suna gararamba a garin Birnin kebbi.
Wannan na kunshe a wata sanarwa da hukumar ta wallafa ranar Asabar 23 ga watan Disamba 2023.
Sanarwar na dauke da cewa:
"ANSAMU KANANAN YARA MATA SU BIYU SUNA GARARANBA A BIRNIN KEBBI
hukumar Hisbah ta samu Yara Yan mata guda biyu Daya Mai suna Aisha lawali jah Yar kauyen magazu unguwar sabon layi dake tsafe local govt zamfara state,
Sai Dayan Kuma Mai suna Nasmatu Abdullahi gwangwala Yar kyauyen kunduttu dake maiyama local govt jihar kebbi
Duk kansu sun zo yawo ragaita ne garin Birnin Kebbi hukumar Hisbah ta jihar kebbi ta zanta da hukumar Hisbah ta zamfara Don gano iyayen Aisha magazu Don sadata dasu
Haka ma hisbah ta zanta da kakan Nasmatu dake kyauyen unguwar kurya ta maiyama shikuma Yana cikin yanayin rashin lafiya da bazai iya zowa ba Don tace babanta ya rasu mamarta na aure barkeji ta jihar sokoto
Allah ya shiryadda zuriar mu yayi Muna tsari ameen".
From ISYAKU.COM