Sabon rikici ya ɓalle a jam'iyyar adawa yayin da aka lakaɗa wa wasu jiga-jigai 2 dukan kawo wuƙa


Rigingimun da suka dabaibaye Labour Party (LP) ta kasa ya ƙara tsanani yayin da aka yi wa wasu shugabanni biyu dukan kawo wuƙa a jihar Edo.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa ranar Jumu'a, manyan jam'an LP guda biyu, Anslem Eragbe, da wani da ba a gano sunansa ba sun ci na jaki hannun wasu mutane. Legit Hausa ya wallafa.

A faifan bidiyon da ke yawo an ga mutanen suna dukan jiga-jigan biyu a wani wuri da ba a bayyana ba amma ana ganin motoci da gidaje a kewayen wurin.

An ga mutane kusan biyar sun taru suna dukan Mista Eragbe da kafafunsu da wasu abubuwa, sun yaga masa tufafin da ke jikinsa farare, sun bar shi da ƙaramin wando.

Shi kuma ɗayan jigon wanda ya sa shuɗin tufafi na zaune a ƙasa wasu mutane sun kewaye shi, Leadership ta ruwaito.

An tattaro cewa sun ziyarci Benin, babban birnin jihar Edo ne domin aiwatar da tsarin ɓangaren LP ta ƙasa karkashin jagorancin Lamidi Apapa, a shirin zaben fidda gwani.

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin LP na jihar Edo, Samson Uroupa, ya bayyana mutanen biyu, waɗanda yace ba mambobin LP bane da mayaudara.

A cewarsa, dukkansu ba su da alaƙa da jam'iyyar LP kuma sun zo ne da nufin haddasa fitina da tada zaune tsaye.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su kama duk wanda ke da’awar wani bangare a jam’iyyar LP, yana mai cewa kotun koli ta warware wannan matsalar.

A kalamansa ya ce:

"Muna ganin idan har yanzu akwai wanda ke da’awar wani bangare a jam’iyyar, to ya kamata jami’an tsaro su kamo irin wadannan mutane domin kotun koli ta yanke hukunci."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN