Yanzu-yanzu: Yan gida daya su 8 sun mutu a hatsarin mota


Wasu mutane takwas da ke hanyarsu ta koma gida domin bikin sabuwar shekara sun mutu a mummunan hatsarin mota a mararrabar Amanwozuzu da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo. 

Lamarin wanda ya afku da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba, ya jefa al'ummar yankin cikin bakin ciki kasancewar mamatan duk yan gida daya ne, rahoton The Nation.

Wasu da hatsarin ya afku a kan idanunsu sun bayyana cewa mahaifin iyalin wanda ke tuka mata da yaransa a cikin wata motar Sienna ya shigi wata babbar mota da ke fake dauke da karafuna. Legit Hausa ya wallafa.

atsarin ya yi muni sosai domin dai karafunan sun tsire gawarwakin mutane da ke cikin motar kuma gaba dayansu suka mutu nan take.

A cewar wanda abun ya faru kan idonsa, jami'an yan sanda da al'ummar yankin sun fasa motar cikin hawaye domin fitar da gawawwakin iyalin.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, jami'an yan sanda daga karamar hukumar Ikeduru sun mika gawarwakin mamatan a dakin ajiyar gawa.

DPO na yankin Ikeduru, Lucky Ahiole, ya fada ma manema labarai cewa an faka motar daukar kayan ne a gefen hanya lokacin da direban Siennan ya yi taho mugama da ita, rahoton Punch.

Ya ce:

“Abin akwai firgitarwa. Mutum takwas sun mutu kuma mun kai su dakin ajiye gawa. Dole muka fasa motar Sienna don fitar da gawawwakin. Karfe ya tsire idanuwansu da jikinsu hatta ga yaran sun mutu.”
Sai dai kuma, masu wucewa sun yi kira ga yan sanda a kan su bincike mamallaki ko direban motar da aka ajiye wanda ke dauke da karafuna don sanin dalilinda na toshe hanya.

Sun ce da a ce direban motar bai yi fakin a hanya ba, da za a iya dakile wannan bala'i.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN