Yadda masu cin naman dan Adam ke karuwa a Kudu


Labarin Aminiya da ya bankado yadda ake cin kasuwar koda ya tayar da kura da kuma janyo hankalin mahukunta kan wannan muguwar harka, wanda hakan ya sa Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate ya tauna aya don tsakuwa ta ji tsoro.

“Dokar kasa ta haramta saye ko sayar da sassan jikin mutum. Saboda haka duk wanda aka kama da laifin saya ko sayar da sassan jikin dan Adam akwai tarar kudi ko dauri a gidan yari ko duka biyu,” in ji Ministan a hirarsa da BBC kan labarin.

Ya ce, likitoci da jami’an tsaro sun fara bincike don gano masu hannu a wannan lamari da Aminiya ta ba da labari tare da tabbatar da cewa an hukunta dukkan gurbatattun asibitocin da aka samu da laifi.

Sai dai labaran wadanda ’yan sanda suka kama bisa zargin tu’ammali da sassan jikin dan Adam da masu cin naman mutane da masu sayarwa domin yin tsafi ya wuce misali.

Daya daga cikin wakilan Aminiya ya ce lamarin ya fi kamari a Kudancin kasar inda yake zaune shi da iyalinsa shekara da shekaru.

Ya ce a Jihar Ogun abubuwan da suka faru dangane da wannan lamari gabanin Kirsimeti ya yi muni.

Ya ce a cikin watan Disamban nan da ke karewa ’ yan sanda a jihar sun kama mutum biyu masu suna Ifedowo Niyi da Akeem Usman bisa zargin kashe wani dalibin Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) mai suna Quadri Salami inda ake zargin sun cire kokon kansa da zira’in hannunsa biyu suka kuma binne sauran jikin cikin a wani rami.

Da take bayyana haka ga ’yan jarida a Hedikwatar ’Yan sandan Jihar da ke Eleweran a Abeokuta fadar Jihar Ogun, kakakin rundunar, SP Omolola Odutola ta ce mahaifin dalibin ne ya kai rahoton bacewar dansa a ofishin ’yan sanda na Kemta a Abeokuta inda nan take jami’an suka fara bincike suka kai ga kama wadanda ake zargi bayan an samu wayar marigayin tare da su.

Ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Abiodun Mustapha Alamutu da kansa ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin da aka tono rubabben jikin dalibin wanda ta ce bincike ya tabbatar da cewa Ifedowo Niyi ya tura Naira 100,000 cikin asusun banki na Akeem Usman a matsayin rabonsa na sayar da sassan jikin dalibin da ake zargin an yi tsafin ‘Awure’ da kokon kansa da zira’in hannayensa biyu.

Kakakin ta ce, tuni aka mika wadanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar (CID) domin ci-gaba da bincike.

A wani labarin, kakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ya bayar da sanarwar kama mutum uku kan zargin cinikin zuciyar wasu mutum biyu.

Da yake bayani kan lamarin, SP Ayuba Umma ya ce, jagoran wadanda aka kama mai suna Moshood Najimudeen ya dauki hayar wani mai suna Adebanjo Wasiu a kan Naira 50,000 don samo masa zuciyar mutum.

Ya ce an kama wadanda ake zargi a yankin Oke-Ola a garin Ago-Iwoye a Jihar Ogun inda aka samu naman zuciyoyin mutum biyu tare da su.

Sai dai wadanda ake zargin sun ce zuciyoyin aladu ne, ba na dan Adam ba.

An mika sassan jiki ga likitoci domin yin bincike.

Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da Shiyya ta Biyu, Muhammed Ali ya shawarci jama’a su rika tona asirin irin wadannan mutane domin kama su da hukunta su.

A Jihar Ogun ’yan makonni kafin Kirsimeti, wakilinmu ya ce, an kama wasu mutum hudu kan zargin cin naman mutum, ciki har da wata mata da hoton bidiyonta daure da ankwa a kafafunta a ofishin ’yan sanda ya karade gari.

Ana zargin ta da jagoransu da cin naman mutum, a yayin holensu a harabar rundunar.

Rundunar ta ce mutanen da ba ta bayyana sunayensu ba, sun hada da wani mai hakar kabari da mai saye da mai sayar da naman mutane.

Bayan zargin cin naman mutum da aka yi masu an kuma zarge su da kasuwancin sassan jikin mutane inda suke sayarwa a kan Naira 10,000 zuwa sama.

Bincike ya nuna an same su da sassan jikin mutum da suka hada da koda da hanta da kayan ciki da suke dafawa suna ci.

Da Aminiya ta tuntubi wasu mazauna jihohin Kudancin kasar nan kan abin ke kawo haka, Sarkin Hausawan Shagamu, Alhaji Inuwa Garba ya ce, “Abin da ke kawo haka shi ne rashin tsoron Allah da son zuciya da son abin duniya.

“Su suke jefa irin wadannan matasa da tsofaffi a irin wannan mummunar dabi’a.”

Alhaji Inuwa Garba, mai shekara 60 kuma haifaffen yankin ya ce babu irin wadannan masu sayar da sassan jikin mutum a garinsa.

A cewarsa, akwai ’ya’yan kungiyoyin asiri masu tsafi da shan jinin mutane da suke yawan fadace-fadace a tsakaninsu da ke kai ga kasha-kashe da kuma kone-konen kadarorin mutanen gari da babu ruwansu.

Sarkin ya dangana yawaitar lamarin ga son kudi da mulki da hassada a matsayin babban musabbabin wannan lamari, kuma zai yi wuyar gaske mahukunta su iya yin maganin matsalar, in ji shi.

“Saboda aikin ’yan sanda kawai shi ne kama wandanda ake zargi da gurfanar da su a gaban kotu.

“Ita kuma kotu hukunci take yankewa ba mai tsanani ba, inda a karshe za ka ga mai laifin ya fito daga gidan yari ya sake komawa kan danyen aikinsa.

“Iyaye suna da muhimmiyar rawar da za su taka awajen magance wannan lamari,” in ji shi.

Ministan Ali Pate baya ga waccan gargadi da kira ga jama’a su taimaka wa jami’an tsaro, ya kuma bayar da lambar wayar tarho da za a iya amfani da ita wajen sanar da mahukunta kan irin wannan lamari don hada karfi da karfe wajen magance matsalar.

Ya ce, “Wannan gwamnati a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba kamar gwamnatocin baya ba ne da suke sako-sako da irin wannan lamari, manufarmu ita ce mu fada kuma mu aiwatar.”

Rahotun Jaridar Aminiya

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN