Shekara 3 bayan ya yi wa yar shekara 4 fy*de a cikin Masallaci Babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 6 ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Yusuf Bako, mai shekaru 50, bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 4 fyade a cikin wani masallaci da ke kan titin Aminu a cikin birnin Bauchi.


 LIB ta ruwaito cewa Bako ya yaudari karamar yarinya zuwa masallaci kuma ya yi mata fyade a cikin Satumba 2020, yayin da ake ci gaba da kullen COVID-19.

 A baya dai an daure Bako sau biyu bisa laifukan fyade makamantan haka amma gwamnan jihar ya yi masa afuwa watanni kadan domin rage cunkoso a gidajen yari da kuma dakile yaduwar cutar Coronavirus.

 Darakta mai gabatar da kara na ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi Barista Sha’awanatu Yusuf, ta tabbatar da hukuncin a wata hira ta musamman da manema labarai a ranar Laraba 27 ga watan Disamba, 2023.


 Ta ce mai shari’a Sa’ad Zadawa na babbar kotu mai lamba 6 ne ya yanke hukuncin a karshen watan Nuwamban wannan shekara bayan sauraron karar daga bangarorin biyu.


 Sha’awanatu ta bayyana cewa wannan hukunci na nuni da kudurin ma’aikatar wajen tabbatar da adalci ga wadanda aka yi wa fyade da kuma tabbatar da ingancin dokar VAPP da ke aiki a jihar.


 Bugu da kari, Daraktan ta bukaci hukumar shari’a ta kasa da ta gaggauta gudanar da shari’ar wadanda ake zargi da aikata laifukan fyade a jihar, tare da sa ran za a ci gaba da hukunta masu laifi.


 Ta yi kira ga iyaye da masu kula da su da su hada kai da hukumomi wajen gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin fyade.


 “Wasu iyaye suna hana ‘ya’yansu, wadanda aka yiwa fyade, fitowa a gaban kotu da ba da shaida,” in ji Sha’awanatu.


 Abin lura a nan shi ne, a shekarar 2022, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya amince da dokar VAPP, wadda ta tanadi hukuncin kisa da daurin rai da rai ga wadanda ake tuhuma da laifin fyade.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN