Kano: Lauyoyin jihohi 19 sun ƙara gano wata matsala a hukuncin tsige Abba, sun bayyana mafita


Ƙungiyar matasan lauyoyin arewa ta soki hukuncin kotun ɗaukaka kara wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Legit Hausa ya wallafa.

Lauyoyin, waɗanda suka fito daga jihohin arewa 19, sun caccaki hukuncin wanda ya bayyana Nasiru Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano, Channels tv ta ruwaito.

Sun kuma bayyana kuskuren da aka samu a sakin layi biyar na cikin kwafin takardun hukuncin a matsayin wanda ba a yafe wa kuma ya jefa ɓangaren shari'a cikin kokwanto.

Mai magana da yawun ƙungiyar matasan lauyoyin arewa, Yusuf Ibrahim, ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Lahadi a Kaduna.

Ya ce hukuncin da aka yanke a zaben gwamnan Kano, ya nuna rashin adalci karara, kuma mafi mahimmanci, zambar siyasa da canza zaɓin da mutanen Kano suka yi.

A rahoton Leadership, Ibrahim ya ce:

"Maganar gaskiya, a yanzu ba ka da tabbacin hukuncin da kotu za ta yanke a kasar nan, ko da kuwa kai masanin shari’a ne, duk iliminka a fannin.”

Bisa haka ƙungiyar, wadda ta kunshi lauyoyi masu zaman kansu, ta sadaukar da kanta kyauta domin taimakawa Gwamna Abba wajen kwato haƙƙinsa a kotun ƙoli.

Ta kuma jaddada kwarin guiwar cewa kotun Allah ya isa zata yi adaci, ta tabbatar da Abba Gida-Gida a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Kano a watan Maris.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN