Rikicin Kano: DSS za su binciki Rabiu Musa Kwankwaso? Bayanai sun fito


Wata Æ™ungiyar yaÆ™i da ta’addanci da ke aiki a Æ™arÆ™ashin Æ™ungiyar National Coalition Against Terrorism (NCAT) ta buÆ™aci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gaggauta gayyatar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ƙungiyar ta buƙaci DSS ta gayyaci Kwankwaso ne domin amsa tambayoyi dangane da zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, da cin zarafin ƴan ƙasa da kuma kai hare-hare kan ɓangaren shari'a. Legit Hausa ya wallafa.

Ƙungiyar ta bayyana fargabar cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, ƙungiyar Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya za ta iya tayar da tarzoma a ƙasar nan biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na tsige Gwamna Abba Yusuf.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, Terrence Kuanum, kodinetan ƙungiyar na ƙasa, ya kuma ƙara da cewa, Kwankwasiyya na shirin kai hare-hare tare da cin mutuncin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, don haifar da tarzoma a Kano da Abuja.

Kuanum ya bayyana cewa tun kafin hukuncin kotun zaɓe da ya tsige Gwamna Abba, ɓangaren shari'a musamman alƙalai suka ria fuskantar barazana daga wajen ƴan Kwankwasiyya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tuni aka fara haka ta hanyar yin zanga-zangar da wasu son tada ƙayar baya suke yi domin nuna adawa da hukuncin kotu na tsige Gwamna Abba.

Ƙungiyar ta ce:

"Ba tare da wata shakka ba, muna kira ga shugaban DSS da ya gaggauta gayyatar Rabi’u Musa Kwankwaso domin yi masa tambayoyi kafin Æ´an Kwankwasiyya su Æ™ona Æ™asar nan."

"A matsayinsa na tsohon Gwamna, tsohon ministan tsaro da kuma Sanata, yana iya haifar da tashin hankali kuma ya jajirce akan yin hakan."

"Muna kuma ba da shawarar a kama tare da yi wa waÉ—annan masu son tayar da hankalin da tuni Mista Kwankwasiyya ya haÉ—a baki da su domin jagorantar tashe tashen hankula a Abuja, Mista Ladipo Johnson, Ladipo Olayoku, Alhaji Abba Kawu, Prince Nwaeze Onu, Tunde Oke, Badmus Kilamuwaye, Olufemi Oguntoyinbo da sauransu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN