Kakakin Majalisar Wakilai ya karanto sunayen sabbin shugabannin kwamitoci 27 da mataimaka


Kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajuddeen, ya karanta sunayen sabbin shugabannin kwamitoci 27 da mataimakansu na majalisar. Legit Hausa ya wallafa.

Kwamitocin sun kunshi guda 26 da ake da su a majalisar wakilai ta ƙasa da kuma ƙarin guda ɗaya da aka raɗa wa sunan, "kwamitin abinci da samar da abinci."

Daily Trust ta tattaro cewa Abbas ya sanar da sabbin shugabannin kwamitocin da mataimakansu a zaman mambobin majalisar na ranar Jumu'a, 1 ga watan Disamba, 2023.

Kakakin ya bayyana sauye-sauyen da aka samu a kwamitocin jim kaɗan bayan kasafin kuɗin 2024 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a zauren majalisar.

Honorabul Abbas ya karanto sunayen kana ya roƙi shugabanni da mataimaka masu barin gado su hanzarta miƙa ragamar kwamitocin ga sabbin da aka naɗa.

Wannan sauye-sauye na zuwa ne yayin da majalisar wakilan ke shirin fara sauraron ma'aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda zasu zo kare kasafinsu.

Da yake jawabi, Abbas ya ce:

"Wannan shi ne jerin sunayen ciyamomin kwamitoci da mataimakansu bayan an gyara su. Akwai buƙatar masu barin gado su mika ragama ga sabbin waɗanda suka maye gurbinsu cikin hanzari."

"Hakan na da matuƙar muhimmanci domin tattabar da zaman da za a fara da ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya ya tafi yadda ya dace."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN