Fankon kwalin kasafin kudi Tinubu ya gabatarwa yan majalisa? Daga karshe gaskiya ta bayyana


Dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Doguwa/Tudun Wada a Kano, Alhassan Doguwa, ya yi watsi da ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa yan majalisa da fankon kasafin kudin shekara mai zuwa. Legit Hausa ya wallafa.

A hirar da aka yi da shi a sashin Hausa na BBC, wani mamba na jam'iyyar adawa ta NNPP, Yusuf Galambi, ya yi zargin cewa babu abin da su ka samu a cikin kwalayen da shugaba Tinubu ya gabatarwa majalisar tarayyar.

Galambi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jigawa ya ce:

Amma da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, Doguwa ya dage cewa yan majalisa sun samu cikakken kunshin kasafin kudin Tinubu kafin jawabin da ya yi a gaban majalisun biyu, rahoton Punch.

Doguwa ya ce:

"Abun da mutane basu sani ba shine cewa tuni Shugaban kasa Tinubu ya gabatar da na'ura na gaba daya kunshin kasafin kudin kafin jawabinsa a gaban majalisar hadin gwiwar."
Ya bayyana ikirarin cewa fankon kwalin kasafin kudi yn majalisar suka samu a matsayin mara tushe balle makama, rahoton The Cable.

Doguwa ya fayyace cewa kamar yadda aka saba, Tinubu ya ba da kwafin jawabinsa tare da na'urar da ke dauke da kwafin cikakken kasafin kudin da yadda za a kashe su.

Dan majalisar ya bukaci a daina juya gaskiya da gangan dangane da gabatar da kasafin kudin da fadar shugaban kasa tayi.

“A daina juya gaskiya, ba mu karbi fankon kwalin kasafin kudin 2024 ba daga hannun Shugaba Tinubu ba,” in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN