An yi kira ga mahukuntan jihar Kebbi bayan Doki ya ci karo da mota a Bayan Kara, an bayyana bukatu 3 a Birnin kebbi {Bidiyo)

 

Wani Doki da babu kowa a kai ya ci karo da wata mota kuma ta buge shi ya fadi a cikin magudanar ruwa a Birnin kebbi. Lamarin ya haddasa tsaikon jama'a da ababen hawa.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bayan Kara da misalin karfe 7:45 na yamma bayan Dokin ya fito da gudu daga filin sukawu ya nufo titi kuma nan take wata mota ta yi karo da shi ya fada cikin magudanar ruwa saboda matsewar, titin ranar Litinin 5 ga watan Disamba.

Titin Unguwar Bayan Kara na fama da hidimar jama'a da ababen hawa wadanda ke kai kawo a takure. Kazalika gefen titi wanda ke makale da magudanar ruwa na fama da rashin inganci duba da yadda gabar titin ke karyewa yana faduwa sakamakon tsayawar motoci kawai.

Tuni al'ummar unguwar Bayan Kara suka sha yin kira ga mahukunta a jihar Kebbi su fadada wannan hanyar tare da inganta magudanar ruwa duba da irin muhimmancin Unguwar Bayan Kara a fannin albarkatun jama'a.

Latsa nan ka kalli bidiyo 
👇👇👇👇

Yadda Doki ya yi karo da mota ya fada cikin magudanar ruwa a Bayan Kara Birnin kebbi. Dalili da ya kamata mahukunta su fadada wannan hanyar saboda da matsewarta

Posted by ISYAKU.COM on Tuesday, December 5, 2023

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN