An gan gawar wani mutum da ba a san ko waye ba an kona shi a shiyyar Takita da ke bayan unguwan Oando a garin Birnin kebbi. Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta sanar da haka ranar Laraba 20/12/2023.
Hukumar ta wallafa cewa:
"ANGA GAWAR WANI MUTUN KONANNA WANDA BA A SAN KO WANENE BA SHIYAR TAKITA BAYAN OANDO GARIN BIRNIN KEBBI
Ansamu rahoton cewar an kashe wani mutun Kuma an konashi a takita bayan oando garin Birnin Kebbi
Ana sa ran ankashe shi fiye da kwana biyu da suka gabata Amma ba a sanar da hukuma ba sai yau laraba 20/12/2023 bayan jikin sa ya lalace kawo yanzu baa iya tantance sanadiyar mutuwar wannan bawan Allah
Bincike Yana kan gudana Don gano musabbabin wannan dayen aikin"
From ISYAKU.COM