Daga karshe Minista ya fadi dalilin da ya sa ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu


Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong ya yi murabus daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.

A cewar wata sanarwa daga kakakinsa, Simon Macham, Lalong ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Legit Hausa ya wallafa.

Ya dauki matakin ne domin ya samu damar darewa kujerarsa a matsayin sanata mai wakiltan Filato ta kudu karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Lalong ya yi murabus ne sakamakon nasarar da ya samu a zaben sanata na ranar 25 ga watan Fabrairu, bayan kotun daukaka kara ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Hukuncin kotun ya sauya sanarwar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a baya, inda ta ayyana Napoleon Bali na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe daga wajen INEC a watan jiya sannan a yanzu ya shirya kama aikinsa na sanata.

Mista Macham ya jaddada cewa zabin ministan na sauka daga mukaminsa na minista abu ne mai matukar nauyi.

Ba a dauki wannan mataki da wasa ba saboda amana da kwarin gwiwar da Shugaba Tinubu ya ba shi.

A baya ministan ya yi aiki a matsayin darakta janar na kwmaitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, inda ya taka muhimmiyar rawar gani wajen nasarar da APC ta samu.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta nakalto, sanarwar na cewa:

Sai dai kuma, bayan tuntuba mai yawa da mai girma shugaban kasa da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummata, ya zama dole gareni in ci gaba da zama a majalisar dattawa don ci gaba da ba da gudummawa ga ajandar sabunta fata na gwamnatin ka da kuma ci gaban dimokuradiyyar mu gaba daya."

Mista Lalong ya yi godiya ga shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin aiki a majalisarsa da kuma irin goyon baya da jagorancin da ya samu a lokacin da yake rike da mukamin minista.

Yayin da yake a majalisar dattawa, ministan ya yi alkawarin biyayya, goyon baya, da bayar da hadin kai ga shugaba Tinubu, domin bayar da gudumawa ga ajandar sabunta fata da kuma ciyar da manufofin jam’iyyar APC gaba don samun hadin kai, ci gaba da wadata a Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa sabon zababben Sanatan ya ziyarci majalisar ne domin mika takardar shaidar cin zabensa da kuma takardun da suka dace ga magatakardar majalisar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN