Jami'in NSCDC ya haddasa hargitsi bayan ya bindige dalibai 2 a makarantar Sakandare a Abuja


Akalla dalibai biyu na wata makarantar sakandare da ba a bayyana ba da ke unguwar Gwarinpa a Abuja, an yi zargin jami’an hukumar tsaro ta NSCDC ya harbe su har lahira.


 Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba yayinda aka tura jami’an NSCDC da ke ofishin babban birnin tarayya Abuja domin samar da tsaro a yayin gudanar da jarrabawar.


 Rikicin ya haifar da hargitsi a kusa da harabar makarantar amma jami’an ‘yan sanda da suka isa wurin sun cafke jami’an NSCDC tare da kwantar da hankula.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, “An samu wani lamari a wata makarantar sakandare.  Nan take muka je wurin, kuma a halin yanzu, ina iya tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin”.


 Adeh ta ce kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Garba Haruna ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin sanin yadda lamarin ya faru.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN