Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗin mace a matsayin shugabar hukumar NIS ta ƙasa


Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da nadin Wura-Ola Adepoju a matsayin kwanturola-janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS). Legit Hausa ya wallafa.

Adepoju ta bayyana hakan ne ga ma’aikatan hukumar NIS yayin faretin babban kwanturola na ƙasa ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, cewar rahoton Premium Times.

A kalamansa, Misis Adepoju ta ce:

"Zaku so sanin cewa cikin ikon Allah da amincewar gwamnatin yanzu, an tabbatar da ni a matsayin babbar kwanturola-janar ta hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS)."

Ta kuma bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a sanar da ranar bikin naɗinta a wannan babban matsayi wanda a yanzu take riƙo.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN