Yadda Yan sanda a Bauchi suka damke barawo da ya saci mota a wani Masallaci a Zariya


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun cafke wani da ake zargin barawon mota ne mai suna Ibrahim Mohammed mai shekaru 25 da laifin satar mota a wani Masallaci a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce jami’an da ke aiki a hedikwatar ‘yan sandan Tilden Fulani sun kama wanda ake zargin da motar da ya sace a kan babbar hanyar da ta hada jihohin Bauchi da Filato.


 PPRO ya bayyana cewa wanda ake zargin wanda ya fito daga Unguwan Gyadi-Gyadi, jihar Kano, amma kuma yana zaune a Gwarinpa, FCT Abuja, ya amsa laifinsa kuma za a mika shi jihar Kaduna domin ci gaba da bincike.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN