Yan Boko Haram sun yi wa ayarin motocin Gwamnan Yobe kwanton bauna, sun bindige dan sanda sun jikkata jami'ai

Illustrative picture

Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da aka raunata wasu guda shida bayan wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun yi wa motocin tawagar rakiyar Gwamnan Yobe kwanton bauna.

Daily trust ta rahoto wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi wa tawagar motocin jami’an tsaron Gwamnan jihar Yobe kwanton bauna a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe dan sanda daya tare da jikkata wasu shida.

 An kai harin ne a hanyar Jakana zuwa Mainok a jihar Borno.

 Rahotanni sun bayyana cewa tawagar jami’an tsaron sun raka gwamnan Maiduguri ne domin halartar taron karo na 24 na jami’ar Maiduguri, inda aka baiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima digirin girmamawa.

 Yayin da tawagar ta koma Yobe, an ce Buni ya tsaya a Maiduguri kafin ya tafi Abuja don wata ganawa a hukumance.

 Da yake tabbatar da harin, mai magana da yawun gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya ce jami’an tsaron sun yi arangama.

 "Sun yi harbe-harbe amma jami'an tsaron da ke rakiyar motocin gwamnan da suka koma Damaturu sun yi musayar wuta da su, amma 'yan sanda uku sun samu raunuka," in ji shi.

 Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin kuma wadanda suka jikkata suna karbar magani.

 Sai dai wata majiyar tsaro daga ayarin motocin ta shaida wa wakilinmu cewa, “Sojojin da ke jagorantar ayarin motocin dauke da Bindigar Motar MRAP da wata mota da ke dauke da ‘yan sanda da DSS aka kai wa hari.

 “Saboda haka, sojojin sun mayar da mumunar martani, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya.  Sai dai abin takaicin shi ne dan sanda daya ya mutu, yayin da sojoji biyu da suka hada da direba, ‘yan sanda uku da DSS daya sun samu raunuka.

 “Jami’an tsaro sun dawo Damaturu, babban birnin jjihar Yobe lafiya, yayin da aka kwashe wadanda suka jikkata da direban motar zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba, amma wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali,” inji majiyar.

 Ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu daga bangaren 'yan ta'adda ba kawo yanzu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN