'Yan ta'adda sun sama da mutane 100 a garin Mutunji da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.
An tattaro cewa ‘yan ta’addan (’yan bindiga) sun kai harin ne a daren Juma’a bayan sallar isha’i. PM News ta rahoto.
Mazauna yankin sun shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ‘yan bindigar sun kasance masu biyayya ga Damina, dan ta’addan da ke yankin. Sun ce ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura inda suka kewaye mutanen kauyen kafin su kai su dajin.
An gano cewa an sace su ne saboda rashin biyan harajin Naira miliyan 50 da mutanen kauyen za su ba Damina.
Babu wata sanarwa daga jami'an tsaro game da harin da aka kai a daren Juma'a a garin Mutunzi kawo lokacin rubuta wannan rahotu.
From ISYAKU.COM