Dakarun sojojin Najeriya da 'yan banga sun ceto wasu mutane shida da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi ranar Juma'a.
Malam Yahaya Sarki, mai ba Gwamna Nasir Idris shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana haka a Birnin Kebbi a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce an kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya kuma an dawo da su ga iyalansu.
“Dakarun Bataliya 1, Dukku Barrack, Birnin Kebbi tare da ‘yan banga sun kai farmaki tsaunin Kogon Damisa da ke kusa da Saminaka a karamar hukumar Shanga, kan iyaka tsakanin Kebbi da Neja a ranar Juma’a.
“Rundunar ta fatattaki ‘yan bindiga da dama tare da ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su.
“An riga an ba da rahoton bacewar wadanda abin ya shafa, yayin da aka sace su da dadewa,” in ji shi.
Sarki ya yabawa kwazon sojojin tare da jaddada kudirin gwamnati na tallafawa hukumomin tsaro a jihar.
From ISYAKU.COM