An kama wani mutum mai shekaru 53 mai suna Usman Tela Ahmadu, dan gudun hijira (IDP) da ke zaune a garin Samunaka a karamar hukumar Yola ta Arewa bisa laifin yin lalata da wata karamar yarinya mai tabin hankali.
Wanda ake zargin dan asalin garin Maiduguri ne a jihar Borno, rahotanni sun ce yana samun kyautuka da tallafin da bai kamata ba daga mazauna yankin.
A cewar ikirari daga wanda ake zargin, ya yi lalata da yarinyar da ke fama da tabin hankali har sau hudu tun farkon shekarar 2021.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya nuna damuwarsa da faruwar lamarin, ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da su da su samar da kayayyakin bukatu ga yaransu don hana su fadawa hannun masu aikata laifuka.
From ISYAKU.COM