A jawabinsa na Æ™arshen mako-mako a fadar Vatican, Fafaroma É—an shekara 86 ya yi kira da a yi addu’a don zaman lafiya, yana mai cewa bangarorin biyu: “Sun sha wahala sosai kuma na ji yadda dukansu suke shan wahala.”
“ A YaÆ™e-yaÆ™e ana yin haka, amma a nan an wuce yaÆ™e-yaÆ™e. Wannan ba yaki ba ne, wannan ta’addanci ne,” ya kara da cewa, ba tare da bayyana ko yana magana ne kan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba ba, ko harin da sojojin Isra’ila suka kaddamar a Gaza a matsayin mayar da martani, ko kuma duka biyun.
Fadar Vatican ta ce a makon da ya gabata Paparoma ya yi fatan nuna "kusancinsa na ruhaniya" yayin ganawar sirri, wanda ta ce zai kasance "na musamman na jin kai".
From ISYAKU.COM