Yadda bacin rai ya sa amarya ta yi ajalin maigida bayan ta kwada masa tabarya a kai


Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta cafke wata matar aure mai suna Biba Mohammed bisa zargin kashe mijinta da tabarya.

 Lamarin ya faru ne a unguwar Barunde da ke cikin birnin ranar Alhamis, 16 ga Nuwamba, 2023.

 Kakakin rundunar, ASP Mahid Muazu Abubakar, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, 2023, ya bayyana cewa an samu kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar Barunde Quarters a Gombe, inda ake zargin an yi kisan kai a unguwar.

 An aika da jami’an ‘yan sanda zuwa wurin, inda suka gano marigayin, Mohammed Maliki, kwance cikin jini.

 Nan take aka garzaya da mamacin zuwa Asibitin kwararru dake Gombe, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

 Bayan wani bincike na farko da aka yi, an kama matar marigayin mai suna Biba Mohammed, bayan ta amsa laifin ta.

 A bayanin da ta yi wa Yan sanda, ta ce ta yi amfani da tabarya wajen buge kansa, wanda a karshe ya kai ga mutuwarsa.

 "A halin yanzu ana binciken shari'ar a SCID kuma za a gabatar da ita a gaban kotu bayan kammala binciken," in ji PPRO.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN