Gwamnatin jihar Legas a karkashin Gwamna Olusola Sanwo-Olu, ta sha alwashin kawo karshen barace-barace a kowane bangare na jihar.
Akalla mabarata 50 a tituna ne aka kwashe daga hanyar a wani samame na musamman karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar matasa da ci gaban jama’a, Mobolaji Ogunlende.
Ma’aikatar tare da hadin guiwar Lagos State task force na jihar Legas ne suka shirya shirin na “Special Rescue Operations” domin tsaftace barace-barace a kan tituna a yankin Lekki a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023.
From ISYAKU.COM