Imam ya zama mutum na farko da ya samu mukamin Farfesa a Rundunar Sojin Najeriya


Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya, NDA, da ke Kaduna ta sanar da ƙarin girma ga Laftanal-Kanal Abubakar-Surajo Imam zuwa matsayin Farfesa a fannin 'Mechatronics Engineering'. Legit Hausa ya wallafa.

Mista Imam shi ne Farfesa na farko daga cikin ma'aikatan da ke aiki yanzu a tarihin rundunar sojojin Najeriya, cewar rahoton Daily Nigerian.

Magatakardan kwalejin, Birgediya-Janar AM Tukur ya sanar da ƙarin girman a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba a Kaduna, rahoton PM News ya tabbatar

Ya ce an amince da ƙarin girman ne yayin taron majalisar zartaswar kwalejin NDA a watan Satumba, kuma ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Oktoban 2022.

Magatakardar ya ce matakin majalisar ya nuna ƙwarin gwiwa da amincewa da gudunmawar da Malam Imam ya bayar ga sashen 'Mechatronics Engineering' na kwalejin.

Ya ce sabon Farfesan ya samar da ayyuka na kwarai tare da tabbatar da ƙwazon da ake sa rai a fagen nasa.

"Wannan ƙarin girman ba wai kawai ya karrama Farfesa Imam ba ne, amma ya nuna jajircewar NDA wajen yarda da yin sakayya kan gudunmawar da aka bayar ta fannin ilmi a cikinta." A cewarsa.

Malam Imam wanda ya fito daga Kankia a Jihar Katsina, ya yi digiri na farko a fannin 'Mechanical Engineering' a jami’ar Bayero da ke Kano.

Ya kuma yi Digiri na biyu a fannin Mechatronics daga jami’ar Newcastle da ke UK, sannan ya yi digiri na uku a fannin Mechatronics da Robotics daga Jami'ar ta Newcastle.

A halin yanzu ya na riƙe da matsayin shugaban, sashen 'Mechatronics Engineering' da daraktan cibiyar 'Centre for Innovation and Innovation' a kwalejin NDA.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN