An hukunta korarren sufeton dan sanda da ke satar makamai daga hedikwatar Yan sandan jihar Neja yana sayar wa yan bindiga


 Kotun Majistare ta Minna ta yanke wa wani korarren Sufeto na Yan sanda mai suna Yahaya Mohammed hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin sata da sayar da Magazin na Ak 47 da harsashi ga wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar.


 Kafin a kore shi Mohammed, shi ne na biyu mai kula da dakin ajiye makamai a hedikwatar ‘yan sandan jihar Neja. Jaridar Vanguard ta wallafa.


 An ce ya hada baki ne da Ndaman Gana wanda kuma jami’i ne mai kula da sashin kula da makamai na rundunar ‘yan sandan jihar domin aiwatar da wannan mugunyar aikin.


 An gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi hada baki da kuma satar Magazin na Ak47 da kuma cinikin haramtacciyar magazine ta Ak47 da harsashi.


 Rahoton ‘yan sanda na farko da aka gabatar a kotu ya bayyana cewa, wasu sahihan bayanai da aka samu daga wata majiya mai tushe daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke karamar hukumar Rafi, Kagara, jihar Neja ta bayyana cewa  wani mutum zai yi jigilar kaya a cikin 'Ghana must go' wanda ake zargin makamai ne zuwa tashar mota ta Kagara. 

"Sakamakon haka Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin kama ku Sufeto Yahaya Mohammed dan sanda wanda a da yake aiki a sashen adana makamai na Rundunar Yan sandan jjhar kuma mai matsayi na biyu a sashen".


 “A yayin binciken ‘yan sanda, kai tsohon sifeton ‘yan sanda ka hada baki da Ndaman Gana jami’in kula da makamai na Yan sandan jihar da ke aiki a sashin Operation OPs Minna, kuma ku biyun kun sace magazin 22 da alburusai 61 na rundunar ‘yan sandan jihar Neja. 


 "Ku biyun ku sayar da kowace magazin akan kudi N1000 kowacce harsashi an sayar da ita akan kudi N650 ga wani kofur Sani Mohammed wanda a da yake aiki a Mopol 12 Minna," in ji rahoton na farko.


 Lokacin da shugabar kotun Majistare Hajiya Fati Umar Hassan ta karanta masa tuhumar, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.


Daga karshe Kotu ta yanke wa Yahaya Mohammed daurin shekara biyu a gidan Yari ko ya biya tarar Naira dubu dai (N100,000)


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN