Kotu ta daure yaron da ya ci zarafin budurcin kananan yara mata masu shekara 5, da 6 a Badariya jihar Kebbi

 

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Birnin kebbi ta samu wani matashi dan shekara 16 Habibu Umar da laifin yin lalata da yara Yan mata kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali.


 Dan sanda mai gabatar da kara  Insp.  Muntari Mati, a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, a wata kara mai lamba BK/538C/223,  ya gabatar da Habibu Umar a gaban kotu bisa tuhuma guda daya na cin zarafi ta lalata wanda ya sabawa sashe na 263 na kundin laifuffukan Penal na jihar Kebbi.


 Habibu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotu, Alkalin Kotun Samaila Kakale Mungadi  don haka ya yanke wa Habibu hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira dubu dari da hamsin (N150,000).


 Zaku iya tuna cewa kafar yada labarai ta yanar gizo isyaku.com ta ruwaito cewa tun farko jami'an tsaron Masarautar Gwandu ne suka kama Habibu Umar wanda hakan ya sa aka kara daukar mataki.


 Bayan an yi masa tambayoyi na farko a Fadar Ubandoman Gwandu, daga baya aka mika shi ga hukumar Hisbah ta jihar Kebbi, bayan da aka yi zargin ya lalata wasu kananan ‘yan mata biyu masu shekaru biyar da shida a wani daji da ke tsakanin unguwar Badariya da Barikin Sojoji a Birnin kebbi a ranar 21 ga Nuwamba 2023. Karanta.  rahoton farko a nan


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN