An kama yaro dan shekara 16 bayan ya yi wa kananan yara mata 2 yan shekara 6, 5 fyade a Badariya jihar Kebbi


An kama wani matashi dan shekara 16 Habibu Umar bisa zargin yi wa kananan yara biyu fyade a unguwar Badariya a Birnin kebbi.


 An kama shi ne da sanyin safiyar ranar Talata 21 ga watan Nuwamba, 2023 bayan da ya rudi kanan yara mata biyu da ke zaune a Badariya zuwa wani daji da ke kusa tsakanin yankin Badariya da barikin sojoji inda ya lalata ‘yan matan biyu masu shekaru 6 da 5 ta hanyar yi masu fyade.


 Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com  ya tattaro cewa Kwamanda Ahmad Waziri, DC Aminu Abdullahi da Samaila Karo Kwamanda Bayan Kara ne suka gudanar da aikin a karkashin kwamitin tsaro da ke aiki karkashin Masarautar Gwandu karkashin jagorancin Alhaji Bello Nahaliku.


 Tun da farko dai kwamitin ya gabatar da wanda ake tuhuma da wadanda aka yi wa fyade a gaban Ubandoma na Gwandu, inda wanda ake zargin ya amince da aikata laifin a fadar bisa radin kansa yayin da ake masa tambayoyi.


 Binciken lafiya na farko da ma’aikacin lafiya daga Cibiyar Kiwon Lafiya ta Kebbi da ke ofishin Hisbah na fadar Ubandoma suka yi, ya tabbatar da an keta budurcin kananan yaran biyu.


 Hakazalika, Gwajin kwayar cutuka da jami'an kiwon lafiya suka gudanar ya nuna wanda ake zargin yana dauke da Hepatitis B, amma yaran basu kamu dacutar ba a sakamakon gwajin farko. Sai dai za a bukaci 'yan matan su maimaita gwajin bayan makonni uku.


 Jaridar isyaku.com ya tattaro cewa an mika karar ga hedikwatar Hisbah ta jihar Kebbi.  Bayan binciken farko da kwamandojin Hisbah suka yi, an mayar da shari’ar ga rundunar ‘yan sandan Najeriya Area command reshen Birnin kebbi domin bincike da gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN